Home Dish Lemon tsamiya, danyar citta da lemon zaki

Lemon tsamiya, danyar citta da lemon zaki

Introduce

Chef :

Khady Dharuna

Lemon tsamiya, danyar citta da lemon zaki

Nayi amfani da ragowar lemon tsamiya da ya rage min, sai na markada lemon zaki na zuba akai ya bada dandano me dadi da ma'ana.#kanostate

Cooking instructions

* Step 1

A sami roba me tsafta a zuba tsamiya sannan a zuba ruwa a wanketa tass, sai a dunka tsamewa ana zubawa a tukunya me tsafta sai a zuba ruwa ya sha kanta a Dora akan wuta har sai ta dahu sai a sauke.

* Step 2

A wanke danyar citta a tabbatar dattin da kasar ya fita, sai a yayyanka kanana a zuba ruwa a markada blender ko a goga da greeter, sannan a zuba ruwa a tace. Dusar zaki iya shanyawa kiyi amfani da ita as kayan kamshi.

* Step 3

Sannan a wanke lemon zaki a bare sai a cire kwallayen da farin tsakiyar.(a kula da cire kwallayen, Idan ba a cire ba lemon zai baki wani dandano me daci Idan an markada). Sai a zuba a blender a markada a tace.

* Step 4

A dauko roba me tsafta a tace tsamiya, sannan a zuba ruwan cittar, a kawo ruwan lemon a zuba, sai a saka kankara daga nan a kawo syrup sugar a zuba, Idan babu a zuba a normal sugar a juya. Za a ji yana kanshi Idan sukari yaji sai a zuzzuba a sha. Idan ba kankara za a iya sakawa a fridge yayi sanyi.

* Step 5

Lemon yanada dadi ga kara lfy.
Image step 5

Note: if there is a photo you can click to enlarge it

10 Pieces Of Expert Nutrition Advice

1. Start Small

2. Fill Your Plate With Beans and Leafy Greens

3. Focus on Adding—Not Subtracting

4. Taste the Rainbow

5. Prioritize Potassium

6. Eat More Plants

7. Focus on Your Immune System

8. Try the Mediterranean Diet

9. Understand the Impact of Food

10. Guard Your Gut

See more
🇻🇳 Việt Nam 🇺🇸 USA

Copyright © 2024 Cookcic