Home Dish Filawa me nama(meat pie)

Filawa me nama(meat pie)

Introduce

Chef :

Mrs Maimuna Liman

Filawa me nama(meat pie)

Ina matukar son meat pie sosai.

Ingredient

Cooking instructions

* Step 1

Da farko za'a tankade filawa a roba,sai a saka sinadarin dandano,a saka bakar hoda a gauraya su,sai a fasa kwai 1 a zuba kadan aciki sai a gauraya su duka su hade,sai a saka ruwa kadan ayi ta murzawa har yayi laushi ya zama ya hade jikinshi baya kama hannu,sai a ajiye shi na minti 10.

* Step 2

A samu dankalin turawa guda 4 a fere sai a gurza shi da abun goge kubewa,haka ma karas,sai a saka mai kadan a abun suyan kwai a juye dankalin da karas aciki sai a gauraya sosai sai yayi laushi,sai a juye dambun naman,a saka yankakken albasa da attarugu da sinadarin dandano a gauraya su hada komai yayi daidai sai a sauke.
Image step 2

* Step 3

Sai a dauko kwabin a gutsira kadan a murza yayi fale-fale sai a saka akan abun shape din meat pie,sai a zuba hadin aciki sai a shafa ruwa a bakin a rufe shi.
Image step 3 Image step 3

* Step 4

Haka za'ayi har a gama,sai a saka acikin abun gashi sai a shafa musu kwai a gasa.
Image step 4 Image step 4

* Step 5

Gashi nan bayan sun gasu kenan.
Image step 5

* Step 6

Za'a iya korawa da ruwan shayi ko lemo me sanyi 😋
Image step 6

Note: if there is a photo you can click to enlarge it

Tag

10 Pieces Of Expert Nutrition Advice

1. Start Small

2. Fill Your Plate With Beans and Leafy Greens

3. Focus on Adding—Not Subtracting

4. Taste the Rainbow

5. Prioritize Potassium

6. Eat More Plants

7. Focus on Your Immune System

8. Try the Mediterranean Diet

9. Understand the Impact of Food

10. Guard Your Gut

See more
🇻🇳 Việt Nam 🇺🇸 USA

Copyright © 2024 Cookcic