Home Dish Teba (tuwon garin kwaki) da miyar agushi

Teba (tuwon garin kwaki) da miyar agushi

Introduce

Chef :

Mrs Maimuna Liman

Teba (tuwon garin kwaki) da miyar agushi

Yana da matukar dadi kuma ga saukin sarrafawa.

Ingredient

Cooking instructions

* Step 1

Da farko a tsince dattin cikin garin sai a zuba shi a tukunya a ajiye,sai a samu wani tukunyan a saka ruwa a ciki a daura a wuta ya tafasa,idan ya tafasa sai a juyé acikin wannan garin a zuba sosai saboda ya ratsa sai a rufe shi kaman na minti bayar, sai a tuka shi a daura a kan wuta à ragé wutan sosai à barshi ya turara,sai a sake tuka shi maikyau a sauke.

* Step 2

(Miyar agushi kuma) a wanke nama da kifi duka a saka su à tukunya a yanka musu albasa da attarugu a zuba aciki,a saka kamshi da sinadarin dandano sai a barsu su dahu sosai suyi laushi,sai a tsayar da ruwan miya a wanke bitter leaf a saka a zuba mishi manja a barshi na minti gama, sai a zuba garin agushin acikin wani roba a yanka albasa manya akai sai a saka mishi dandano a gauraya sai a diga ruwa kadan a gauraya shi sosai saboda jikinshi ya hade,sai a juye acikin miyan a barshi ya dahu.

* Step 3

Idan ruwan ya janye sai a saka ganyen ugu a barshi ya turaru kaman minti biyar sai a sauke miya ta hadu,za'a iya ci da ko wani irin tuwo.

Note: if there is a photo you can click to enlarge it

Tag

10 Pieces Of Expert Nutrition Advice

1. Start Small

2. Fill Your Plate With Beans and Leafy Greens

3. Focus on Adding—Not Subtracting

4. Taste the Rainbow

5. Prioritize Potassium

6. Eat More Plants

7. Focus on Your Immune System

8. Try the Mediterranean Diet

9. Understand the Impact of Food

10. Guard Your Gut

See more
🇻🇳 Việt Nam 🇺🇸 USA

Copyright © 2024 Cookcic