Home Dish Tsiren naman karamar dabba

Tsiren naman karamar dabba

Introduce

Chef :

Khady Dharuna

Tsiren naman karamar dabba

Yanada dadi gashin sosai. Gashi baya cin lokaci wajen gasuwa, nan da nan zaki gama. #namansallah

Ingredient

Tafarnuwa

domin bukata

Cooking instructions

* Step 1

A sami nama me kyau gurin tsoka inda babu jijiya, sai a yayyanka shi madaidaita, a wanke shi tass a caccaka masa wuka sbd Idan anyi hadi ya rasa cikin, a tsane ruwan

* Step 2

Sannan a saka fennenl seed, a jajjaga tafarnuwa Idan ana bukata, curry, spices, garin citta, Maggie, bama, jajjagen tarugu da albasa kadan, da garin yaji shima kadan. Sai a jujjuya sosai har koina yaji sai a saka a fridge na tswwon awa 1 da rabi.

* Step 3

Sai a jika thinken yin tsire a ruwa na mintuna 30 sannan a cire. A yayyanka albasa yankan manya, tattasai ma haka, tumatir da Koren tattasai duk ayi musu yankan manya

* Step 4

Sai a dauko tsinken a soka albasa, sannan nama, sannan Koren tattasai sannan nama sannan albasa sai tumatir, sai Jan tattasai haka za ayi tayi har a gama.
Image step 4 Image step 4

* Step 5

Sai a kunna abin gashi Idan ya yi zafi sai a dauko tsiran a jera sannan a yaryada mai akai sai a barshi ya gasu, a dunga juyawa akai akai sbd Kar ya kone. Anayi ana yaryada mai har a gama. Za aji yana kamshi.
Image step 5 Image step 5 Image step 5

* Step 6

Idan aka tabbatar ya gasu sai a cire a saka a kwano ko faranti.
Image step 6

* Step 7

A ci da duminsa yafi dadi. Za a iya saka Wa a tsakiyar bread a ci. Shima akwai dadi.
Image step 7 Image step 7

Note: if there is a photo you can click to enlarge it

10 Pieces Of Expert Nutrition Advice

1. Start Small

2. Fill Your Plate With Beans and Leafy Greens

3. Focus on Adding—Not Subtracting

4. Taste the Rainbow

5. Prioritize Potassium

6. Eat More Plants

7. Focus on Your Immune System

8. Try the Mediterranean Diet

9. Understand the Impact of Food

10. Guard Your Gut

See more
🇻🇳 Việt Nam 🇺🇸 USA

Copyright © 2024 Cookcic