Home Dish Alale da kunun gyada

Alale da kunun gyada

Introduce

Chef :

Mrs Maimuna Liman

Alale da kunun gyada

#breakfastideacontest

Ingredient

Cooking instructions

* Step 1

Da farko za'a jika wake a surfa shi hancin ya fita a wanke shi a jika.

* Step 2

Sai a yanka albasa,attarugu da tattase a wani roba ajiye a gefe,idan waken ya jika sai a tsiyaye ruwan kai a juye su albasa akai a markada.

* Step 3

Idan an markada shi sai a saka mishi seasonings da spices nashi a zuba man ja,a zuba ruwa daidai kaurin da akeso a gauraya shi,sai a shafa man ja a cikin ledan da za'a daure sai ana zuba kullin à ciki ana daurewa.

* Step 4

Sai a saka ruwa a tukunya a kan wuta idan ya tafasa sai a dauka kullin da aka daure a leda a saka su a cikin ruwan har su nuna.
Image step 4

* Step 5

(For d kunu) a samu markadadden gyada wanda yayi laushi sai a zuba mishi ruwa aciki a dama shi ko ina ya hadu ya gaurayu kaman ruwa sai a tace a tukunya a daura tukunyan a wuta.

* Step 6

A zuba couscous din kunu a ciki a gauraya a barshi har kunun ya tafasa shima couscous din yayi laushi.

* Step 7

Sai a yanka lemon tsami a matse ruwan a tace shi,sai a tankade flour kasan acikin ruwan lemon tsamin a gauraya shi sosai idan kunun ya nuna sai a sauke shi a kasa a zuba wannan lemon da flour din aciki a gauraya har kunun yayi kaurin da akeso.

* Step 8

Kunu da alale sun gamu sai ci,za'a iya ci da mai da yaji ko man ja,pepper soup,sauce etc.

Note: if there is a photo you can click to enlarge it

Tag

10 Pieces Of Expert Nutrition Advice

1. Start Small

2. Fill Your Plate With Beans and Leafy Greens

3. Focus on Adding—Not Subtracting

4. Taste the Rainbow

5. Prioritize Potassium

6. Eat More Plants

7. Focus on Your Immune System

8. Try the Mediterranean Diet

9. Understand the Impact of Food

10. Guard Your Gut

See more
🇻🇳 Việt Nam 🇺🇸 USA

Copyright © 2024 Cookcic