Home Dish Burodi me kwakwa

Burodi me kwakwa

Introduce

Chef :

Khady Dharuna

Burodi me kwakwa

Burodin yayi dadi sosai, kasancewar shine gwajin farko sai gashi yayi kyau yayi laushi ga kamshi. Musamman ma aka ci shi da lemon kwakwa. #bakebread

Ingredient

Food ration :

Cin mutum 3 yaw

Cooking time :

1 and half hrs

Cooking instructions

* Step 1

A sami roba me tsafta a tankade fulawa a ciki.
Image step 1

* Step 2

Sannan a zuba sukari akai
Image step 2

* Step 3

Sai a zuba madarar gari akai
Image step 3

* Step 4

Sannan a kawo yeast a zuba akai
Image step 4

* Step 5

Sai a kawo gishiri shima a zuba, sai a jujjuya su hade guri daya.
Image step 5

* Step 6

Bayan nan sai a FASA kwai akai a juya
Image step 6

* Step 7

Sannan a kawo madara me dumi a zu akai a kwaba, da ya fara haduwa sai a saka butter a juya sosai a kuma saka butter din har ta kare. Za a ga ya hade jikinta sai a rufe a ajiye a GU me dumi domin ya tashi.
Image step 7

* Step 8

Idan ya tashi za a ga ya ninka na farkon a girma
Image step 8

* Step 9

Sai a kuma bugawa sosai a tabbatar ya kuma hade jikinsa, a sake rufewa a bashi mintuna 10 sannan a dauko a kuma bugawa a murza shape din da ake so. Sai a shafa butter a abin gashi a jejjera biredin akai. A barshi zuwa mintuna 5 za a ga ya sake tashi.
Image step 9

* Step 10

Daga nan sai a FASA kwai a shafa ruwan kwan a jikin biredin.
Image step 10

* Step 11

Sai a kawo kwakwa a cire bayan ta a wanke ta tass sannan a gogata, sai a zuzzuba akan bread din
Image step 11

* Step 12

A kunna oven a Dan yi zafi sai a rage wutar a saka kwanan gashin, a barshi ya gasu a hankaki kar a cika wuta kum. Idan ya gasu za aji yana kamshi me dadi sai a cire.
Image step 12

* Step 13

A barshi ya Dan huce.
Image step 13

* Step 14

Za a iya cinsa hakanan ko da lemo ko da shayi
Image step 14

* Step 15

Ni dai da lemon kwakwa na ci nawa dadi kan dadi kenan.
Image step 15 Image step 15

Note: if there is a photo you can click to enlarge it

10 Pieces Of Expert Nutrition Advice

1. Start Small

2. Fill Your Plate With Beans and Leafy Greens

3. Focus on Adding—Not Subtracting

4. Taste the Rainbow

5. Prioritize Potassium

6. Eat More Plants

7. Focus on Your Immune System

8. Try the Mediterranean Diet

9. Understand the Impact of Food

10. Guard Your Gut

See more
🇻🇳 Việt Nam 🇺🇸 USA

Copyright © 2024 Cookcic