Home Dish Dambun shinkafa me naman kaza

Dambun shinkafa me naman kaza

Introduce

Chef :

Khady Dharuna

Dambun shinkafa me naman kaza

Dambu abinci ne da mutane da yawa Suke sonsa yasa na sarrafashi ta hanyar hadashi da naman kaza a ciki. Ku gwada Ku ban labar Harda Santi. #kanostate

Cooking instructions

* Step 1

Bayan an barzo mini shinkafa sai na diba daidai yanda zaici steamer din, na wanke da ruwa na tsane ruwan. Sannan na zuba soyayyen mai kamar cokali 3 na sa Maggie shima ba da yawa ba da Dan gishiri kadan na jujjuya na jefa icen kirfa sannan na juye a cikin steamer din dama na Dora akan wuta ruwan ya yi zafi sai na sa buhu a saman na rufe da murfin sannan na Dora Abu me nauyu.
Image step 1

* Step 2

Bayan ya turaru sai na juyeshi a babbar tukunya na marmasashi ya zama babu gudaje ya yi warawara.
Image step 2

* Step 3

Sannan na zuba magi, curry, spices hade da dakakkiyar gyada, da tafarnuwa Idan ana bukata na juya
Image step 3

* Step 4

Sai na zuba yankakkiyar albasa, jajjagen attaruhu da albasa hade da zogale shima na juya
Image step 4

* Step 5

Daga nan na kawo tsokar kaza wadda na tafasata da kayan kamshi da Maggi nayi mata yankan kanana banda kashi na zuba na juya.
Image step 5

* Step 6

Sannan na kawo ruwan tafashen kazar da na'a na'a na zuba akai na juya suka hade na dandana naji komai yaji sai na mayar cikin steamer din ya karasa turaruwa. Idan yayi zakiji kamshi na musamman yana tashi sai ki juye a roba ko tukunya.
Image step 6

* Step 7

Sai ki zuba soyayyen mai Wanda yaji albasa akai ki cire icen kirfa din sannan ki juya sai a zuba a ci da zafinsa yafi dadi. Kyanta akwai lemon tsamiya me hadin danyar citta a kusa....
Image step 7

Note: if there is a photo you can click to enlarge it

10 Pieces Of Expert Nutrition Advice

1. Start Small

2. Fill Your Plate With Beans and Leafy Greens

3. Focus on Adding—Not Subtracting

4. Taste the Rainbow

5. Prioritize Potassium

6. Eat More Plants

7. Focus on Your Immune System

8. Try the Mediterranean Diet

9. Understand the Impact of Food

10. Guard Your Gut

See more
🇻🇳 Việt Nam 🇺🇸 USA

Copyright © 2024 Cookcic