Home Dish Lemon Zobo me inibi Danye.(zobarodo)

Lemon Zobo me inibi Danye.(zobarodo)

Introduce

Chef :

Khady Dharuna

Lemon Zobo me inibi Danye.(zobarodo)

Zobon yanada dadi na musamman, ga kayan hadin da akayi amfani dasu duk Suna daga cikin abubuwan da suke kara lafiya. Sai an jarraba za aji dadinsa sosai. #zoboreciepcontest

Cooking instructions

* Step 1

Ga dukkan kayan da za ayi amfani da zu nan.
Image step 1

* Step 2

A sami roba me tsafta a zuba zobo a ciki sannan a zuba ruwa a girgijeshi sai a dunga tsanewa ana zubawa a tukunya me tsafta, amfanin yin hakan sabida tsakuwa ko kasa su fita. Idan an gama sai a zuba ruwa daidai misali.

* Step 3

A zuba kanumfari, masoro, kirfa, cardamom, danyar citta a gogata da manyan gida a zuba. Sannan a wanke na'a na'a a zuba akai sai a kara ruwa ya hau kan zobon sannan a Dora akan wuta a jefa yar kansa aciki sabida tsamin ya ragu a barshi yayi ta dahuwa Idan ya dahuwa sai a sauke.
Image step 3

* Step 4

A feraye bayan beetroot a yayyankashi kanana, a raba inibi 2 a cire kwallan sai a hada su guri daya a markada. Idan sun markadu sai a tace.
Image step 4

* Step 5

A wanke cucumber ma a yayyankashi kanana itama a markada ta, sai a tace a ajiye a gefe

* Step 6

A samu babban Abu a tace zobon sai a kara ruwa a zuba ruwan beetroot da inibi hade da ruwan Cucumber a juya da majuyin katako sabida Kar yayi karni. A zuba sukari a juya sosai sannana a saka flavour Idan ana bukata a juya har sai yayi yanda ake so. A jefa kankara a ciki ko a saka a fridge yayi sanyi.
Image step 6

* Step 7

A zuzzuba a Kofi sai a saka yankakkiyar gurjin bature jikin kofin a kawo ganyen na'a na'a a sakala a jikin gurijin Baturen, a saka wata a cikin lemon. Sannan na jug din a saka inibi a gefe a kawo ganyen na'a na'a a sa a jiki.
Image step 7

* Step 8

Sannan ayi kwalliya da wasu daga cikin kayan hadin, yanada dadi kuma yana kara lfy
Image step 8

Note: if there is a photo you can click to enlarge it

10 Pieces Of Expert Nutrition Advice

1. Start Small

2. Fill Your Plate With Beans and Leafy Greens

3. Focus on Adding—Not Subtracting

4. Taste the Rainbow

5. Prioritize Potassium

6. Eat More Plants

7. Focus on Your Immune System

8. Try the Mediterranean Diet

9. Understand the Impact of Food

10. Guard Your Gut

See more
🇻🇳 Việt Nam 🇺🇸 USA

Copyright © 2024 Cookcic