Home Dish Gasashshen meat pie

Gasashshen meat pie

Introduce

Chef :

Khady Dharuna

Gasashshen meat pie

Gasashshen meat pie, kasancewar anfi yin soyayye yasa na kawo muku yanda akeyin gasashshe. Yanada mutukar dadi sosai.

Ingredient

Food ration :

Guda 9 manya

Cooking time :

minti 30mintuna

Cooking instructions

* Step 1

A zuba mai a kasko Idan ya dau zafi sai a zuba albasa, a juya a zuba ruwa cokali 1, a motsa minti 2 sai a zuba attaruhun a motsa, a zuba naman shima a motsa na minti 3 sai a juye dankalin a ciki a saka magi, curry parsley da spices a juya a bashshi ya karasa sai a sauke.
Image step 1 Image step 1

* Step 2

A tankade fulawa a zuba butter, magie guda 2, bakar gode, gishiri kadan da spices a juya sai sun hade guru daya sannan a zuba ruwan dumi a kwaba. Har sai ya hade jikinsa
Image step 2

* Step 3

A yayyanka kwabin, sannan a barbada fulawa a abin murji a dunga fadadawa sai a saka a abin dannewa a shafa ruwa a bakin sannan a zuba hadin a danne.

* Step 4

A shimfida foil paper a kan farantin gashi sai a shafa butter sai a dunga jera meat pie din akai
Image step 4

* Step 5

A kada kwai sannan a yi amfani da brush na kitchen a shafa a saman meat pie din.
Image step 5

* Step 6

A kawo ridi a barbada a saman meat pie din.
Image step 6

* Step 7

A kunna oven a barshi yayi zafi sai a rage wutar a saka tray din a ciki a barshi ya gasu sai an ga ya fara zama ruwan Zuma sai a cire.
Image step 7

* Step 8

A juye a kwano. An gama
Image step 8 Image step 8

Note: if there is a photo you can click to enlarge it

10 Pieces Of Expert Nutrition Advice

1. Start Small

2. Fill Your Plate With Beans and Leafy Greens

3. Focus on Adding—Not Subtracting

4. Taste the Rainbow

5. Prioritize Potassium

6. Eat More Plants

7. Focus on Your Immune System

8. Try the Mediterranean Diet

9. Understand the Impact of Food

10. Guard Your Gut

See more
🇻🇳 Việt Nam 🇺🇸 USA

Copyright © 2024 Cookcic