Home Dish Shinkafa da wake(garau garau)

Shinkafa da wake(garau garau)

Introduce

Chef :

Khady Dharuna

Shinkafa da wake(garau garau)

Khady Dharuna #garaugaraucontest Garau garau tana daya daga cikin abincin hausawa da akafi so, wasu don kwadayi sukeyi Wanda mafi yawa anfiyi don abincin yau da kullum. Haka zalika yarana Suna sonta sosai...

Ingredient

Cooking instructions

* Step 1

A gyara salak a wankeshi dattin ya fita sannan a yayyanka shi yanda ake so, sai a kuma zuba masa ruwa a sa gishir a wanke sosai dattin ya fita sai a tsane a kwalanda, a wanke tumatir, gurijin bature a yayyanka, a kankare bayan karas sai a goga shi, dukkansu a ajiyesu guri guda.
Image step 1

* Step 2

A Dora ruwan zafi a kan wuta, a tsince wake a cire dattin, Idan ruwan yayi zafi sai a zuba a rufe tukunyar ruf yanda iska bazata Shiga ba. Idan ya fara laushi sai a wanke shinkafa a zuba a Dan saka gishiri kadan a barsu su dahu tare.
Image step 2

* Step 3

Idan sun dahu sai a zuba ruwan dumi a tace a mayar kan wuta sai a rage wuta don ya turaru kamar na Minti 5 sai a sauke.

* Step 4

A zuba mai a kwanon suya sai a yayyanka albasa me Dan yawa sannan a Dora akan wuta Idan albasar ta fara yin ja sai a sauke.

* Step 5

A zuba garau garau din a mazubi sai a zuzzuba kayan hadin. A ci da duminta.
Image step 5

Note: if there is a photo you can click to enlarge it

Tag

10 Pieces Of Expert Nutrition Advice

1. Start Small

2. Fill Your Plate With Beans and Leafy Greens

3. Focus on Adding—Not Subtracting

4. Taste the Rainbow

5. Prioritize Potassium

6. Eat More Plants

7. Focus on Your Immune System

8. Try the Mediterranean Diet

9. Understand the Impact of Food

10. Guard Your Gut

See more
🇻🇳 Việt Nam 🇺🇸 USA

Copyright © 2024 Cookcic