Home Dish Jalof din makaroni kala 2 hade da dankalin turawa

Jalof din makaroni kala 2 hade da dankalin turawa

Introduce

Chef :

Khady Dharuna

Jalof din makaroni kala 2 hade da dankalin turawa

Khady Dharuna. #kanostate. Kasancewar yanayin zafi akeyi, abinci dole sai an hada da Mara nauyi gudun chushewar ciki. Girkinnan akwai dadi sosai....

Ingredient

Cooking instructions

* Step 1

A Dora mai akan wuta a yanka albasa, Idan yayi zafi sai a zuba makaroni a soya har ta zama ruwan Zuma sai a kwashe a kwalanda.

* Step 2

A feraye dankalin turawa a yi masa manyan yanka a ajiye a gefe.

* Step 3

A wanke nama sai a zuba a tukunya a tafasa da kayan dandano hade da kayan kamshi da albasa.

* Step 4

A kankare bayan Kara's a wanke sai a yayyanka yankan kwance. A hada da mulmulallen wake a wanke a ajiye a gefe, a jajjaga tarugu da albasa da tafarnuwa Idan ana bukatar a ajiye a gefe

* Step 5

Dora tukunya me tsafta akan wuta zuba mai kadan da albasa Idan yayi zafi zuba naman da aka tafasa har ya soyu sama sama, zuba jajjagen a ciki a motsa, Minti 5 zuba Karas da mulmulallen wake a sake motsa wa rufe Na mintuna 5 sannan a zuba ruwa daidai yanda zai dafa makaronin, a kawo dankalin da aka yanka a zuba a ciki a rufe.

* Step 6

Idan ya tafasa zuba makaroni a ciki zuba kayan dandano, kayan kamshi, bay leaf, na'a na'a, a motsa sannan a rufe.

* Step 7

Idan ta kusa dahuwa sai a watsa yankakkiyar albasa a ciki su karasa dahuwa tare

* Step 8

Za aji tana kamshi sai a sauke a zuzzuba a mazubi.
Image step 8

Note: if there is a photo you can click to enlarge it

10 Pieces Of Expert Nutrition Advice

1. Start Small

2. Fill Your Plate With Beans and Leafy Greens

3. Focus on Adding—Not Subtracting

4. Taste the Rainbow

5. Prioritize Potassium

6. Eat More Plants

7. Focus on Your Immune System

8. Try the Mediterranean Diet

9. Understand the Impact of Food

10. Guard Your Gut

See more
🇻🇳 Việt Nam 🇺🇸 USA

Copyright © 2024 Cookcic